<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>144</hymn_number>
<title>Allah. Ya Ba Mu Hasken Rai Domin Mu Haskaka LW144</title>
<lyrics>[V1]
 1) Allah. ya ba mu hasken rai domin mu haskaka,
 Jama'a duk su gaskata Yesu Ɗan Allah ne.

[V2]
 2) Shi kuwa ya nuna ƙaunarsa a cikin hasken nan.
 Ya aiko Ɗansa, tilo ne, Ya sauko duniyan nan.

[V3]
 3) Wanda ya ƙyale hasken nan, ya fi son duhunsa.
 Ba zai ga fuskar Allah ba sai cikin fushinsa.

[V4]
 4) Yanzu ku tuba, bi shi dai, domin ku sami rai.
 Ba wata hanyar ceto fa, sai Yesu shi kaɗai.

[V5]
 5) Ya Yesu, ba mu ikonka mu furta ƙaunarka,
 Mu shaida. kai ne cetonmu da ƙarfin zuciya.</lyrics>
</song>